Jummaʼa 24 Yuli 2026 - 16:51
Makarantar Zainabiyya | Rawar da Ummu Kulthum (A.S.) Ta Taka Wajen Farkar da Al'umma da Shimfiɗa Hanyar Tashin Mutanen Kufa (2)

Hauza/ Lokacin da wata mace fursuna ta tsaya a gaban mutanen Kufa tana magana da irin wannan ƙarfin hali da jarumtaka, ta aika da saƙo zuwa tarihi cewa: Juyin Imam Husaini (A.S.) bai ci gaba da rayuwa da takobin maza kawai ba, har ma ya ci gaba ta hanyar kalmomin bayyana gaskiya da ruhin jarumtar matan Ahlul Baiti (A.S.).

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza |

Wannan shi ne ci gaban tattaunawa kan rawar da Sayyida Ummul Kulthum ta taka bayan waƙi'ar Karbala da abin da ya biyo baya.

Jawabin Sayyida Ummu Kulthum (A.S.) a Kufa da tasirinsa wajen wayar da kai

Bayan waɗannan abubuwa, a cikin tsoffin littattafan tarihi masu tushe, ba a samu rahotanni masu yawa game da Sayyida Ummu Kulthum (A.S.) ba, sai dai abin da aka ruwaito game da bankwanan da Imam Husaini (A.S.) ya yi da matan gidansa, inda aka ambaci sunayen: "Ya Zainab" da "Ya Ummu Kulthum" a matsayin mutane biyu daban-daban.

Wannan yana ƙara tabbatar da cewa Sayyida Zainab (A.S.) da Sayyida Ummu Kulthum (A.S.) mutane biyu ne masu zaman kansu.

Daga cikin manyan wuraren da aka fi ganin tasirin Sayyida Ummu Kulthum (A.S.) akwai jawabinta da ta yi a Kufa bayan faruwar Ashura.

Sayyid bn Tawus a cikin littafinsa mai suna "Al-Luhuf" ya kawo wannan jawabi, inda ya ruwaito shi daga Zaid bn Musa bn Ja'afar (A.S.), daga Imam Sadik (A.S.), ta hanyar silsilar Imamai (A.S.).

Akwai yiwuwar Imam Sadik (A.S.) ya karɓi wannan ruwaya ne daga mahaifinsa Imam Baƙir (A.S.).

A cikin wannan jawabi, Sayyida Ummu Kulthum (A.S.) ba kawai ta tsawatar wa mutanen Kufa saboda rashin taimakon Imam Husaini (A.S.) ba ne, har ma ta taɓo zukatan waɗanda suka yi shiru suka bar wannan babban laifi ya faru.

Ma'anar kalamanta ita ce: "Shin kun san wanda kuka kashe saboda rashin cika alkawarinku? Shin kun san jinin wane kuka zubar?"

Waɗannan tambayoyi sun kasance hanya ta tayar da hankalin mutane, karya shirun da ya mamaye al'umma, da kuma tada tunanin nauyin da ke kansu.

Tasirin zamantakewa da tarihi na wannan jawabi

Muhimmancin wannan jawabi ba ya tsaya ne kawai ga kyawawan kalmomi da ƙarfinsa ba, har ma yana bayyana ne ta hanyar tasirin da ya yi a cikin al'umma da tarihi.

Lokacin da wata mace fursuna ta tsaya a gaban mutanen Kufa tana magana da irin wannan ƙarfin hali da jarumtaka, ta aika da saƙo zuwa tarihi cewa: Juyin Imam Husaini (A.S.) bai ci gaba da rayuwa da takobin maza kawai ba, har ma ya ci gaba ta hanyar kalmomin bayyana gaskiya da ruhin jarumtar matan Ahlul Baiti (A.S.).

Daga nan ne ake fahimtar cewa jawabai na Sayyida Ummu Kulthum (A.S.) da Sayyida Zainab Kubra (A.S.) a Kufa sun kasance daga cikin manyan abubuwan da suka taimaka wajen farfaɗo da tunanin jama'a.

Waɗannan jawabai sun kasance daga cikin abubuwan da suka haifar da motsin neman ɗaukar fansar jinin Imam Husaini (A.S.), kamar Tawwabun (Masu tuba) daTawayen Mukhtar

A zahiri, waɗannan manyan matan sun yi magana da lamirin al'umma da suka yi shiru, suka dasa tsaba na adawa da zalunci a cikin tarihin ɗan Adam.

Hana wulakanta matsayin matan Ahlul Baiti (A.S.)

Bayan wannan lamari, an ruwaito wata tattaunawa tsakanin Sayyida Ummu Kulthum (A.S.) da mai gadin Ibn Ziyad.

Ta nemi a sanya kawunan shahidai masu tsarki a gaban ayarin fursunonin, domin hankalin mutane ya karkata ga kawunan shahidai maimakon kallon matan Ahlul Baiti (A.S.).

Wannan hali yana nuna cewa iyalan Manzon Allah (S.A.W.A) ko da suna cikin matsanancin wahala da rauni na zahiri, sun ci gaba da kula da mutuncinsu, darajarsu da kiyaye alfarmar iyalin Annabi (S.A.W.A).

Ba su bari tsananin yanayin bauta da wahala ya hana su kare martabar Ahlul Baiti (A.S.) ba.

Hana karɓar sadaka a Kufa

Lokacin da aka shigar da fursunonin Karbala zuwa Kufa, wasu daga cikin mutanen Kufa sun raba abinci da dabino ga yara ƙanana na ayarin.

A cewar ruwayar Allama Majlisi a cikin littafin "Biharul Anwar", Sayyida Ummu Kulthum (A.S.) ta karɓe waɗannan abubuwa daga hannun yaran, ta jefar da su ƙasa, sannan ta yi kira: "Ya mutanen Kufa! Lallai sadaka haramun ce a gare mu."

Ma'ana: "Ya mutanen Kufa, ba ya halatta mu karɓi sadaka."

Wannan magana ta nuna ƙarfi, juriya da tsayin daka na gidan Ahlul Baiti (A.S.).

Saƙon wannan aiki shi ne ko da yake muna cikin yunwa, muna cikin ƙunci, kuma muna ƙarƙashin ikon maƙiyi, addini da mutunci ba za su yarda mu watsar da darajarmu ba.

Za mu iya jure yunwa, wahala da ma mutuwa, amma ba za mu karɓi abin da shari'a ta hana mana ba.

(Za a ci gaba a Sashe na 3.)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha